Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Kaddamar Da Cibiyar Watsa Labarai Ta CMG A Yankin Pudong Na Shanghai
2020-11-11 19:16:47        cri

 

 

A jiya Talata, an kaddamar da cibiyar watsa labarai dangane da bikin cika shekaru 30 da fara raya yankin Pudong da aiwatar da manufar bude kofa a yankin dake birnin Shanghai, ta babban rukunin gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG. Mataimakin darektan sashin kula da harkokin watsa labarai na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kana shugaban CMG, Mista Shen Haixiong, da Madam Zhou Huilin, babban jami'in mai kula da aikin watsa labarai ta birnin Shanghai, sun ziyarci cibiyar, tare da duba yadda ake shirye-shiryen aikin watsa labarai dangane da bikin cika shekaru 30 da fara raya yankin Pudong.

Bayan da ya saurari bayanan aikin da ma'aikatan cibiyar watsa labarai suka gabatar, Mista Shen ya ce, kasar Sin ta cimma nasarar shawo kan yaduwar cutar COVID-19, da zama babbar kasa daya tilo dake ci gaba da samun karuwar tattalin arziki, a karkashin jagorantar kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Haka kuma, yadda aka gudanar da cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 19 lami lafiya, ya kara nuna damar kaddamar da wani sabon tsarin raya kasa ta zamani mai bin tsarin siyasa na gurguzu. Bisa la'akarin da wannan yanayin da ake ciki, aikin watsa labarai game da bikin cika shekaru 30 da raya yankin Pudong yana da muhimmanci matuka. Saboda haka, ya kamata sassa daban daban na CMG su yi kokarin kirkiro sabbin fasahohi, tare da tsara wasu shirye-shirye masu inganci, musamman ma shirye-shirye da za su dace da yanayin yaduwar bayanai a shafin yanar gizo ta Internet, don tabbatar da aiwatar da aikin watsa labarai masu alaka da bikin cika shekaru 30 da fara raya yankin Pudong cikin nasara. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China