Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Metkurban Metsedi: Ana adana masallacin Id Kah da kyau a Xinjiang
2020-11-10 14:18:13        cri

Metkurban Metsedi, wani musulmi ne da ke zaune a matsugunin Mubanqiao a unguwar Laochengqu, a gundumar Yutian da ke yankin Hetian a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin.

Dangane da labarun da kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya suka bayarwa cewa, an rushe masallacin Id Kah a Xinjiang, Metkurban Metsedi ya ce, karya ce suka yadawa. Yana zaune ne a kusa da masallacin na Id Kah. Kuma shi da abokan sa sun san wannan masallaci tun daga lokacin yarintar su. Tsawon tarihin masallacin ya wuce shekaru 800.

Ya ce gwamnatin kasar Sin ta mayar da shi a matsayin muhimmiyar dukiyar kasa. Ta zuba makudan kudade wajen yi masa kwaskwarima. Don haka ana adana masallacin da kyau, kana ana amfani da shi yadda ya kamata. Ba wani labari na rushe wannan masallacin na Id Kah a yanzu.

Metkurban Metsedi bai gane sosai ba, dangane da dalilin da ya sa kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya ke cewa, an rushe masallacin na Id Kah. Ya nuna cewa, idan kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya sun nuna musu kulawa sosai, to, za su zo garinsu, su gani da idanunsu. Ta haka za su san hakikanin abubuwa, ko ba haka ba? (Tasallah Yuan )

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China