Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci kasar Amurka da ta daina tsoma baki a harkokin Hong Kong
2020-11-10 19:31:38        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, mista Wang Wenbin, ya furta a yau Talata cewa, kasar Sin ta bukaci kasar Amurka da ta gaggauta daina tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong na kasar Sin, ta kuma soke takunkumin da ya saka wa wasu jami'an kasar Sin 4. Kasar Amurka ta dauki wannan mataki ne saboda yadda kasar Sin take aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong. Dangane da lamarin, Wang ya ce, Amurka tana yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma yin haka ya keta ka'idojin kasa da kasa.

Ban da wannan kuma dangane da zargin da kasar Kanada ta yi wa kasar Sin wai tana kama jama'ar kasar Kanada yadda ta ga dama, Mista Wang Wenbin ya ce, an kama wani dan kasar Kanada ne saboda zarginsa da neman kawo illa ga harkokin tsaron kasar Sin. Yayin da a daya bangare kuma, kasar Kanada ta tsare 'yar kasar Sin, Madam Meng Wanzhou, har fiye da kwanaki 700, duk da cewa, ba ta keta dokokin kasar Kanada ba. Kakakin kasar Sin ya ce kasar Sin tana kalubalantar kasar Kanada da ta nuna shaidu don daidaita batun da ya shafi Madam Meng, ta kuma daina rudin jama'a. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China