Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara karfin farfado da tatalin arzikin duniya
2020-11-09 20:03:57        cri

 

 

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana kudirin kasarsa na yayata gina tattalin arziki mai salon bude kofa tare da kara sanya kuzari ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Wang Wenbin wanda ya bayyana haka Litinin din nan, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, ya ce ma'aikatar cinikayya da babbar hukumar kwastam ta kasar, sun fitar da wasu alkaluma a baya-bayan dake nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya kama hanyar farfadowa. Yana mai cewa, a halin yanzu matakan kandagarki da hana yaduwar cutar COVID-19 da kasar ta aiwatar, sun haifar da manyan sakamako, kana yadda tattalin arzikin kasar ya farfado da yadda jama'a ke tafiyar da harkokinsu a rayuwa, sun nuna juriya da karfin tattalin kasar Sin.

Manyan hukumomin kudi na duniya, kamar asusun bayar da lamuni na duniya, sun yi hasashen cewa, kasar Sin ce kadai cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, za ta samu bunkasar tattalin arziki a wannan shekara. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China