2020-10-15 10:37:13 cri |
Kwalejin nazarin sakwanni da sadarwa ta kasar Sin ce ta fitar da wannan rahoto, bayan nazartar halin bunkasuwar kasashe da yankunan tattalin arziki na yanar gizo mafi karfi a duniya su 47, inda aka gano cewa, a shekarar 2019, yawan kudin dake shafar wadannan kungiyoyi ya kai kimanin dala triliyan 31.8, adadin da ya karu da kashi 5.4% bisa na makamancin lokaci na 2018, matakin da ya fi GDPn duniya da kashi 3.1% a wannan lokaci.
Idan an mai da hankali kan karfin tattalin arziki ta yanar gizo, Amurka tana sahun gaba a duniya, inda yawan kudin dake shafar wannan fanni a Amurka a shekarar 2019 ya kai dala triliyan 13.1. Kana kasar Sin na biye da ita a matsayi na biyu, inda kudin da ya shafi wannan fanni a kasar ya kai dala triliyan 5.2.
Kaza lika, Jamus da Japan da Birtaniya suna kan matsayi na 3 zuwa 5. Yawan kudin da wadannan kasashe dake sahun gaba a duniya daga matsayi na 1 zuwa 5 ke shafa a wannan fanni ya kai kashi 78.1% bisa na dukkanin kasashe ko yankuna mafi karfin tattalin arziki ta yanar gizo a duniya su 47. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China