Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kayayyakin da aka sayar a kasar Sin a watan Satumba ya karu da karu 3.3
2020-10-19 11:41:05        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin, ta sanar Litinin din cewa, kayayyakin bukatun yau da kullum da aka sayar a kasar a watan Satumba, ya karu da kaso 3.3 kan makamancin lokaci na bara.

An samu wannan karuwar ce, bayan ci gaban da aka samu a karon farko kan muhimman kayayyakin yau da kullum a watan Agustan wannan shekara, inda ya karu da kaso 0.5 cikin 100 kan na lokacin bara.

An kuma samu karuwar kaso 0.9 cikin 100 a rubu'i na uku na wannan shekara, kan sayar da kayayyakin na yau da kullum, karuwa ta farko da aka samu cikin watanni uku uku a wannan shekara. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China