Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Alkaluman yawan hajojin da ake kaiwa mutane inda suke bukata sun karu a watan Oktoba
2020-11-09 10:49:08        cri
Alkaluman kididdigar kayayyakin sayayya da ake kaiwa mutane inda suke bukata na kasar Sin, sun karu a watan Oktoba, idan an kwatanta da na watan da ya gabaci hakan. A cewar hukumar lura da safarar wannan rukuni na kayayyakin sayayya ta kasar Sin, alkaluman sun daga zuwa kaso 108.6 % a watan da ya gabata, karin da ya kai na kaso 0.5% kan na watan Satumba.

Hukumar ta kuma ce, ta tattara wadannan alkaluma ne daga bayanan hada hadar kamfanonin da suke gudanar da kai kayayyaki ga masu sayayya, alkaluman da kuma suka kasance bangare na harkokin kasuwancin su.

Bisa kididdigar, fannin kasuwanci na yankunan karkarar kasar shi ne kan gaba, wajen yawan hajojin da aka kaiwa masu sayayya a watan na Oktoba, idan an kwatanta da na watan da ya gabace shi, sakamakon farfadowar tattalin arzikin da kasar ta samu.

Kaza lika alkaluman sun nuna yadda harkokin kasuwanci masu nasaba da wannan fanni suka koma daidai da yadda suke, a makamancin lokaci na shekarar da ta gabata. A fannonin kamfanonin sarrafa hajoji da na ba da hidima kadai, an samu karuwar kaso 111.9% da kaso 109.9%. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China