Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana kokarin farfado da tattalin arzikin Afirka a yayin da ake yaki da cutar COVID-19
2020-11-08 19:08:15        cri

 

 

Yaduwar cutar COVID-19 ta haddasa raguwar tattalin arzikin Afirkam amma kasashen nahiyar Afirka suna kokarin farfado da tattalin arzikin Afirka a yayin da suke yaki da cutar.

A halin yanzu, yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a nahiyar Afirka yana raguwa idan an kwatanta da adadi mafi yawa da aka samu a tsakiyar watan Yuli. Bisa kididdigar da cibiyar yaki da cuttuttuka masu yaduwa ta nahiyar Afirka ta gabatar, an ce yawancin kasashen Afirka sun riga sun zarce lokacin samun yawan mutane masu kamuwa da cutar mafi yawa. Tare da sassauta yanayin tinkarar cutar, dukkan kasashen Afirka suna kokarin farfado da tattalin arzikinsu.

 

A shekarun baya bayan nan, an samu saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka, amma sakamakon barkewar cutar COVID-19, suna fuskantar karin matsaloli masu dimbin yawa a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'ummarsu. Alal misali, wasu kasashen yammacin Afirka kamar su Najeriya da Guinea da Cote d'Ivoire da sauransu suna fuskantar tashe-tashen hankulan siyasa da rikice-rikice, wadanda suke kara tsananta matsalolin zamantakewar al'ummar kasashen yayin da suke kokarin tinkarar cutar COVID-19 da kuma matsalolin rashin guraben ayyukan yi da talauci a sakamakon cutar. Amma kasashen Afirka ba su gaza imaninsu na farfado da tattalin arzikinsu ba. Ga kasar Najeriya, da Habasha, sun yi kwaskwarima kan sha'anin samar da makamashi da sadarwa, sannan kashi 25 cikin dari na kamfanonin Afirka sun gaggauta inganta fasahohin sadarwa don kara zuba jari ga wannan fanni. Kasashen Kenya da Tanzania sun yarda da kamfanonin zirga-zirgar jiragen saman fasinja na ketare su koma kasashensu domin kokarin farfado da sha'anin yawo bude ido.

Akwai doguwar tafiya ga kasashen Afirka wajen farfado da tattalin arzikinsu a yayin da suke kokarin yaki da cutar COVID-19, ya kamata dukkan kasashen Afirka su sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki mai dorewa da kuma kara karfinsu na tinkarar kalubale da hadarori a fannoni daban daban. (Zainab Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China