Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazarin Allurar Rigakafin Cutar COVID-19 Ba Gasa Ba Ce
2020-10-02 17:32:47        cri

A halin yanzu, ana ci gaba da fuskantar matsalar yaduwar cutar COVID-19 a kasashen duniya, allurar rigakafi kan cutar tana da muhimmanci matuka ga dukkanin bil Adama wajen dakile yaduwar cutar a duniya bai daya. Shi ya sa, gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa, da ma kamfanonin duniya suka dukufa wajen karfafa hadin gwiwarsu a fannin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19. Amma, a halin yanzu, akwai wata kasa dake neman nuna iko kan amfani da allurar rigakafi da kamfanonin kasashen ketare suka samar, da bata sunan sauran kasashen duniya cewa, wai suna mai da allurar rigakafi a matsayin makami na siyasa.

A wannan lokaci mai muhimmanci da ake dukufa wajen yaki da cutar, yadda wannan kasa take neman siyasantar da batun allurar rigakafi ya kawo barazana ga kasashen duniya ta fuskar kiwon lafiyar al'ummominsu.

Tabbas, allurar rigakafi za ta kasance abin da dukkanin bil Adama dake rayuwa a duniya za su iya amfana, ta yadda za ta ba da kariya ga al'ummomin kasa da kasa, a don haka, bai kamata ta kasance makamin da wasu kasashe za su yi amfani da ita wajen bata sunan wasu kasashen duniya ba. A yayin taron kolin allurar rigakafi na kasa da kasa da aka yi a watan Yuni na bana, an yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa da su hada kai domin tattara kudaden samar da allurar rigakafi ga al'ummar duniya. Kana, hukumar lafiyar duniya ta WHO ta sha yin kira ga kasashen duniya da su kaucewa yin fito na fito kan batutuwan dake shafar nazari da samar da allurar rigakafi, ya kamata su karfafa hadin gwiwa, domin fuskantar kalubaloli tare, ta yadda za a gaggauta ayyukan samar da allurar rigakafi kamar yadda ake fata.

Lamarin da ya nuna fatan gamayyar kasa da kasa, wato yin hadin gwiwa da nuna aldaci a fannonin nazari da samar da allurar rigakafin cutar COVID-19, domin kare moriyar kasa da kasa yadda kamata. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China