Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai kamata a saka batun siyasa cikin annobar COVID-19 ba
2020-10-10 16:09:07        cri

Tun farko bullar annobar mashako ta COVID-19, har yanzu, akwai wasu 'yan siyasar kasar Amurka wadanda suka yi biris da gaskiyar abubuwan da suka faru, har suna kara yada rade-radi kan kasar Sin da nufin cimma muradunsu na siyasa da shafawa gwamnatin kasar Sin bakin fenti. Wani dan jam'iyyar Republican a kwamitin kula da harkokin diflomasiyya na majalisar wakilan Amurka, wato Michael McCaul ya bullo da wani rahoto kwanan nan, inda ya yi karya da yada jita-jita kan kasar Sin. Kamar yadda malam Bahaushe kan ce, rashin sani ya fi dare duhu.

A cikin rahoton da Michael McCaul ya bullo da shi, ya ce, wai kasar Sin ta kasa wajen koyon darasi daga yaduwar annobar SARS, har ma ta boye ainihin halin da ake ciki tun farkon bullar cutar COVID-19. Amma gaskiyar abun shi ne, a matakin farko na bullar cutar, gwamnatin kasar Sin ta kafa tsarin ko-ta-kwana domin tinkarar ta, kuma ba tare da wani jinkiri ba ta soma aikin nazarin kwayar cutar. A cikin kwanaki 8, Sin ta tabbatar da kwayoyin halittar cutar, kana a kwananki 16, ta yi nasarar samar da sinadarin dake tantance kwayar cutar. Sin ta gabatar da rahoto dangane da yaduwar cutar ga kungiyar WHO da sauran wasu kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da kaddamar da matakai masu tsauri domin hana yaduwar cutar.

Wata karya ta daban da Michael McCaul ya yi ita ce, kungiyar lafiya ta duniya wato WHO tana yunkurin kare kasar Sin, har ma ta boye wasu muhimman bayanai dangane da yaduwar cutar. Amma sanin kowa ne, WHO kungiyar kasa da kasa ce mai kwarjini da kwarewa a fannin kiwon lafiya. Tun bayan barkewar cutar, WHO da kasar Sin sun rika hadin-gwiwa da tuntubar juna, har ma kasar Sin ta gayyaci kwararrun jami'an WHO domin su tattauna da takwarorinsu na kasar Sin kan asalin kwayar cutar, abun da ya shaida cewa Sin babbar kasa ce dake sauke nauyin dake wuyanta. Amma me kasar Amurka ta yi? Gwamnatin kasar ta gaza wajen kandagarkin yaduwar cutar, har ta dora laifi kan sauran wasu kasashe, da kin biyan kudin memba a WHO, daga baya a watan Yulin bana, ta sanar da cewa, za ta janye daga WHO a shekara mai zuwa.

A nasa bangaren, babban darektan kungiyar WHO Mista Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, saka batun siyasa cikin annobar COVID-19 na haifar da babbar barazana ga duk duniya, inda ya yi kira ga kasa da kasa su zama tsintsiya madaurinki daya domin neman mafita.

Ba wani mutum ko wata kasa da ta kirkiro annobar COVID-19. Kasar Sin da sauran kasashe dukkansu suna jin radadi a jikinsu saboda yaduwar cutar, amma tana kokarin hada kai da sauran kasashe domin ganin bayan ta. Idan an dorawa kasar Sin laifin yaduwar cutar, ita Amurka fa? An samu rahoto na farko na wanda ya kamu da cutar kanjamau wato AIDS a Amurka, har ma tana ci gaba da bazuwa a fadin duniya, ko za mu iya dorawa Amurka laifin haka?

Amurka tana fama da cuta, me ya sa take son kasar Sin ta sha magani? Muna kira ga gwamnatin Amurka ta daina nuna taurin-kai, da bambancin ra'ayi, musamman ma ta dakatar da saka batun siyasa a cikin ayyukan shawo kan annobar COVID-19, ta hada kai da kasar Sin a zahirance, domin bada gudummawa tare ga ayyukan dakile yaduwar cutar a duk fadin duniya baki daya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China