Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasar Amurka wadanda suka tsunduma kasar cikin mawuyacin hali ina hankalinku ya tafi?
2020-10-10 21:17:58        cri

A makon da ya shige, matsakaicin yawan karuwar mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ya zarce 46000 a kowace rana a kasar Amurka. Har ma fadar White House ta zama wurin da cutar ta zama ruwan dare. Rahotannin da kamfanin ABC na Amurka ya ruwaito sun ce, zuwa ranar 7 ga wata, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya haura zuwa 34, ciki har da shugaba Donald Trump. A nasa bangaren, fitaccen kwararre kan takaita cututtuka masu yaduwa na Amurka, Anthony S. Fauci, ya tabbatar da cewa, akwai yaduwar cutar mai tsanani a fadar White House. Har ma ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta gamu da matsalar, wato daya daga cikin manyan jami'an tsaron gabar tekun Amurka ya kamu da cutar, al'amarin da ya sa aka killace sauran wasu manyan jami'an rundunonin sojan kasar a gida.

Kamar yadda malam Bahaushe kan ce, munafuncin dodo ya kan ci mai shi, wato 'yan siyasar Amurka sun girbi abun da suka shuka. Hakan na tabbatar da cewa, manufar gwamnatin Amurka na dakile yaduwar cutar ta gaza kwata-kwata. Shahararriyar mujalla a fannin aikin likita mai suna The New England Journal of Medicine ta wallafa wani sharhi kwanan nan, inda ta ce, kasar Amurka ba ta ci jarrabawar da annobar COVID-19 ta yi mata ba, su 'yan siyasar kasar ne suka tsananta halin da kasarsu take ciki.

Amma ga al'ummar Amurka, lokaci mafi muni bai zo ba har yanzu. Mista Anthony S. Fauci ya yi gargadin cewa, idan ba'a dauki matakan hana yaduwar cutar yadda ya kamata ba a lokacin kaka da na sanyi, adadin mace-mace sakamakon cutar zai haura zuwa dubu 400. Shin da gaske 'yan siyasar Amurka ba su tausayawa al'ummar kasar? Shin da gaske za'a canja irin wannan masifa zuwa kisan kiyashin da gwamnatin kasar ta amince da shi, kamar abun da jaridar Washington Post ta ce?(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China