Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Habasha ya ce batagari ba za su gujewa shara'a ba yayin da ake ci gaba da aikin sintirin soji a Tigray
2020-11-08 16:32:51        cri
Firaministan kasar Habahsa Abiy Ahmed, ya nanata cewa, batagari ba za su iya kaucewa fuskantar shara'a ba yayin da ake tsaka da aikin sintirin sojoji a galibin yankunan shiyyar arewacin kasar ta gabashin Afrika.

A ranar Laraba ne firiminista Abiy Ahmed ya bada umarnin gudanar da ayyukan sintirin sojoji domin yakar 'yan tawaye masu fafutukar kwatar 'yan yancin al'ummar yankin Tigray wato TPLF, dake jihar Tigray a arewacin kasar, inda suke mayar da martani kan sansanin dakarun sojojin gwamnatin kasar wadanda suka kaddamar da hari kansu a wannan rana.

A sakon da ya wallafa a shafin twitter ranar Asabar, Abiy Ahmed ya ce, dukkan batagari ba za su taba gujewa hukuncin doka ba, inda ya bukace su da su nemi sulhu ta hanyar tattaunawa.

Ahmed, wanda kuma shi ne babban kwamandan dakarun sojojin kasar Habasha, ya jaddada cewa, babban burinsa shi ne kawo karshen aikata laifuka da aka jima ana aikata su, tare da binciko dukkan daidaiku da kungiyoyin dake da hannu domin hukunta su bisa tanadin dokar kasar.

A cewarsa, kasar Habasha tana kokarin neman cimman nasarar kafa gwamnatin demokaradiyya karkashin tsarin dokokin kasar. Ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta cigaba da bin dukkan makatan da dokar kasa ta amince da su wajen kiyaye zaman lafiyar kasar da bin hanyar tsarin demokaradiyya da kuma gujewa bin manufofin baragurbin 'yan siyasa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China