Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sudan da Habasha sun ziyarci yankunan masanaantu da Sin ta gina
2020-11-02 09:29:31        cri

Firaministan Habasha, Abbiy Ahmed da shugaban gwamnatin riko na kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, sun ziyarci yankunan masana'antu na Adama da kuma na Gabas dake kasar Habasha, wadanda kasar Sin ta gina.

A cewar ofishin Firaministan Habasha, yayin ziyararsu a yankin masana'antu na Adama, shugabannin biyu sun ga yadda ake samar da makarin baki da hanci na yaki da cutar COVID-19.

Yayin ziyararsu a yankin masana'atu na Gabas dake yankin karkarar birnin Addis Ababa kuma, sun ga yadda ake samar da magunguna da iskar da marasa lafiya ke shaka, a wata cibiyar hada magunguna ta kasar Sin dake harabar yankin.

Tun cikin watan Oktoban 2018, kasar Habasha ta kaddamar da yankin masana'antu na Adama, dake kudu maso gabashin birnin Addis Ababa, wanda ke da nisan kilomita 74 daga birnin.

Yankin wanda kamfanin gine-gine na kasar Sin wato CCECC ya gina, wani bangare ne na katafaren shirin gwamnatin Habasha na sauya fasalin tattalin arzikin kasar da ya dogara kan ayyukan gona, ta yadda zuwa 2025, zai mayar da hankali kan ayyukan masana'atu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China