Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun halaka fararen hula a kalla 32 a yammacin kasar Habasha
2020-11-03 10:11:53        cri
Hukumar kare hakkin bil-Adama ta kasar Habasha (EHRC) ta sanar jiya Litinin cewa, wasu mahara sun kaddamar da hari a jihar Oromia ta kasar Habasha, harin da ya yi sanadiyar rayukan mutane a kalla 32.

Hukumar wadda majalisar dokokin kasar ta kafa, ta bayyana cewa, maharan sun nufi 'yan kabilar Amharas ne, kabila ta biyu mafi girma a kasar Habasha, wadanda ke zaune a matsugunai guda uku. Maharan sun fito da mutanen ne daga gidajensu, su kuma kai su wata makaranta, kana suka kashe su.

A cewar hukumar EHRC, wata kungiyar masu dauke da makamai, da marasa makamai ne suka kaddamar da hare-haren na ranar Lahadi, da yawansu ya kai 60 a yankunan Gawa-Kanka, da Gilla-Gongola, da Seka-Jerbi dake shiyyar Wollega, bayan da aka janye sojojin gwamnatin tarayya daga yankunan da kusan tsakar ranar Lahadi.

Lamarin da ya faru a ranar Lahadin, shi ne na baya-bayan nan, a kiyashi mafi muni a kasar ta Habasha, cikin makonni hudu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China