Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministar lafiyar Habasha ta yabawa masanaantar samar da kayan gwajin cutar COVID-19 da Sin ta gina
2020-10-08 16:33:01        cri

 

Ministar lafiyar kasar Habasha Lia Tadesse, ta yabawa kasar Sin bisa kaddamar da masana'antar samar da kayayyakin gwajin cutar COVID-19 da ta gina a kokarinta na tallafawa kasar ta gabashin Afrika wajen yaki da cutar COVID-19.

A wata hira da ta yi kwanan nan, Tadesse ta ce, kasancewar aikin gwaje gwaje shine kashin bayan yaki da annobar ta COVID-19, kaddamar da masana'antar zai yi matukar taimakawa kokarin da kasar Habasha ke yi wajen yaki da cutar COVID.

Masana'antar samar da kayayyakin gwajin cutar COVID-19 ta BGI a Habasha, an gina shi ne a yankin masana'antu na Bole Lemi dake bayan garin birnin Addis Ababa, babban birnin kasar ta Habasha, wanda firaministan kasar Abiy Ahmed ya kaddamar a watan Satumbar da ya gabata.

Kasar Habasha tana fatan masana'antar samar da kayan gwajin cutar ta COVID-19 za ta bada gudunmawa wajen rage makudan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen sayo kayayyakin gwajen gwajen daga kasashen katare.

Tadesse tace, masana'antar samar da kayayykin gwajin cutar COVID-19 ta hadin gwiwa ce tsakanin gwamnatin kasar Habasha da kamfanin BGI Genomics Co. Ltd na kasar Sin, ana sa ran za ta dinga samar da kayayyakin gwajin kimanin miliyan 10 a duk shekara, lamarin da zai taimakawa Habasha, da shiyyar gabashin Afrika, har ma da nahiyar Afrikan baki daya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China