Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 1.85
2020-11-08 15:34:50        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar a ranar Asabar cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a nahiyar ya kai 1,855,396.

Kwararriyar hukumar dakile yaduwar cutukan ta bayyana cikin sanarwar cewa, adadin mutanne da cutar ta kashe a Afrika ya kai 44,471 ya zuwa yammacin ranar Asabar.

Yayin da mutanen da suka warke daga cutar ta COVID-19 adadinsu ya kai 1,555,271 a fadin nahiyar, a cewar Afrika CDC.

Kasashen Afrika da cutar COVID-19 tafi shafa su ne Afrika ta kudu, Morocco, Masar, da Habasha, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Afrika CDC ta ce, shiyyar kudancin Afrika ne annobar COVID-19 ta fi shafa ta fuskar yawan mutanen da suka kamu da kuma mutanen da cutar ta kashe. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China