Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika CDC: Yawan masu COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 1.78
2020-11-02 09:35:54        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce, yawan mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 1,784,083.

Hukumar dakile cutukan ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar cewa, adadin mutanen da cutar ta kashe ya kai 42,869 ya zuwa yammacin ranar Lahadi.

A jimlace, mutane 1,457,764 ne suka warke daga annobar ta COVID-19 a fadin nahiyar ya zuwa yanzu, kamar yadda hukumar dakile yaduwar cutukan ta sanar.

Kasashen Afrika da cutar COVID-19 ta fi shafa ta fuskar yawan mutanen da suka kamu da cutar sun hada da Afrika ta kudu, Morocco, Masar, Habasha, da Najeriya, kamar yadda alkaluman Africa CDC suka nuna.

Shiyyar kudancin Afrika ne inda cutar COVID-19 ta fi yiwa illa ta fuskar yawan masu kamuwa da cutar da kuma yawan mutanen da cutar ta hallaka. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China