Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun yaki da COVID-19 na AU zai kafa gidauniyar neman dala miliyan 300 don yaki da annobar
2020-10-18 16:01:48        cri
Asusun kungiyar tarayyar Afrika AU mai yaki da annobar COVID-19 zai kaddamar da gidauniyar neman kudi dala miliyan 300 domin taimakawa shirin yaki da annobar COVID-19 a Afrika, kungiyar AU ta sanar da hakan.

Shi dai asusun na yaki da COVID-19 na AU, muhimmin jigo ne wajen tsara dabarun yaki da annobar a nahiyar Afrika, a ranar Asabar ya sanar da cewa zai kaddamar da asusun neman taimakon dala miliyan 300, wanda za a yi amfani da su wajen yaki da annobar.

Kungiyar ta Afrika ta ce, taron neman kudaden ta shafin intanet, wanda hukumar gudanarwar AU tare da hadin gwiwar bankin Afrexim za su kaddamar a ranar 24 ga watan Oktoba, za a nemi tallafin ne daga kamfanoni masu zaman kansu na Afrika, da gwamnatoci, da sauran masu bada taimako, domin a tabbatar da nahiyar ta cimma nasarar dakile wannan annoba dake zama barazana ga duk duniya.

AU ta nanata cewa, shirin yaki da annobar COVID-19 a nahiyar ya tara kudi dala miliyan 44, ya jaddada cewa, shirin neman tara kudaden ta intanet wani muhimmin bangare ne wajen kara wayar da kai game da asusun yaki da annobar COVID-19 na kungiyar AU. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China