2020-11-06 15:26:37 cri |
Bekri Yaqub mai shekaru 71, shi ne shugaban kwamitin kula da masallacin Yanghang dake birnin Urumqi a jihar Xinjiang ta kasar Sin. Dangane da wani labarin da kafofin yada labarai na kasashen ketare suka yada, cewar, wai ana rushe masallatai a jihar Xinjiang, malam Bekri Yaqub ya ce, bai taba jin irin wannan labarin ba.
Ya ce, a jihar Xinjiang, akwai masallatai da dama da aka gina tsakanin shekarun 1980 zuwa shekarun 1990, ko kuma kafin wannan lokaci, kuma galibinsu tsoffi ne, wasu kanana ne kuma sun lalace, wasu kuma babu gyara. Idan ana ruwan sama ko iska, kusan ba a iya aiwatar da harkokin Ibada a cikin wadannan masallatai, wasu lokuta ma, idan aka yi girgizar kasa, mutanen dake ciki ko wadanda ke kusa da matallatan su kan fuskanci hadari.
Don haka, cikin 'yan shekarun nan, wasu gwamnatocin sassan jihar sun fara gyara wasu tsoffin masallatai bisa bukatun musulmai na wurin, ko kuma gina sabbin masallatai a wuraren da masallatansu ba su da inganci.
Bugu da kari, ya ce, an gina masallacin Yanghang a shekarar 1897, ba kawai Musulmai na kabilar Uygur da kabilar Hui da sauransu su kan yi salla a masallacin ba, har ma, akwai wasu Musulmai na kasashen ketare da su kan zo nan. Cikin 'yan shekarun nan, bisa taimakon da gwamnatin wurin ta samar musu, harkokin masallacinsu na ci gaba da samun kyautatuwa, dukkanin Musulman da suka zo domin yin salla sun gamsu sosai. (Mai Fassawara: Maryam Yang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China