Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shatar Zunon: Ina Son Bakin Gida Da Ketare Su Dandana Ainihin Abincin Jihar Xinjiang
2020-11-03 11:10:02        cri

Sana'ar Shatar Zunon mai dakin cin abinci a yankin Gaochang dake birnin Turpan na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, na samun bunaksuwa yadda ya kamata yauzu, amma tsattsauran ra'ayi ya taba kawo masa babbar illa.

Shatar Zunon ya tuna cewa, lokacin da yake makarantar midil ya yi mu'ammala da wasu masu tsattsauran ra'ayin addini, har ba ya son shiga makaranta, ya kuma kalli bidiyon ta'addanci, sannu a hankali ya fara nuna kiyayya ga sauran mabiyan addinai. Shatar Zunon ya ce, bayan ya shiga cibiyar koyar da ilmin sana'o'i a wurin, ya fahimci cewa, tsattsauran ra'ayi na lahanta rayuwarsa matuka.

A cibiyar, Shatar Zunon ya koyi fasahar dafa abinci. Bayan ya kammala karatunsa kuma, sai ya yi sha'awar bude dakin cin abinci, amma ba shi da kudi a waccan lokaci. Jami'an kauyensa sun taimaka masa wajen samun rancen kudi da zabar wurin gina dakin cin abinci da gyara shi.

Ya zuwa yanzu, Shatar Zunon ya biya dukkan rancen kudin da ya karba daga banki, ya kuma sake gyara gidansa. Yana farin ciki sosai don samun zaman rayuwa mai wadata kamar mutanen birane.

Yankin Turpan shaharraren birni ne ta fuskar yawon bude ido, Shatar Zunon na shirin shiga harkokin yawon shakatawa a gidajen manoma a birnin, don baki daga gida ko ketare su iya dandana ainihin abincin jihar Xinjiang. Ya yi imanin cewa: "Sana'ata za ta samu ci gaba kuma zaman rayuwata zai kyautatu nan gaba saboda himma da gwazo da nake yi." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China