Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun yaba da gudummawar kayayyakin yaki da COVID-19 da kasar Sin ta samar musu
2020-11-05 10:59:13        cri
Kasashen Afirka sun yaba da ma mika godiyarsu ga gwamnatin kasar Sin, bisa taimakon kayayyakin yaki da annobar COVID-19 da ta baiwa mata da kananan yara da baligai a kasashen nahiyar

Gwamnatoci da jama'a daga bangaorin rayuwa daban-daban a Afirka, sun bayyana cewa, a lokacin da kasashen nahiyar ke fama da karancin kayayyakin yaki da annobar, kasar Sin ta magance matsalolin sufuri na kasa da kasa da ma isar da kayayyakin yaki da annobar zuwa kasashe 53 dake nahiyar Afirka a kan lokaci, matakin da ya taimakawa mata da kananan yara da ma baligai dake nahiyar, magance matsalolin da suke fuskanta a lokacin da ake fama da annobar.

Ita dai wannan annoba, ba ta san iyakar kasa ba, taimakon juna da hadin gwiwa tsakanin kasashe, ita ce hanya daya tilo ta ganin bayanta.

kasar Sin ta shiga hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da wannan annoba, da ma baiwa kasashe da dama a duniya taimako, ciki har da kasashen Afirka, abin da ke nuna cewa, kasar Sin kasa ce da ta damu da jin kan bil-Adama da ruhin hadin gwiwa.

A kwanakin nan ne, dukkan kayayyakin lafiya na yaki da annobar COVID-19 da gwamnarin kasar Sin ta baiwa mata da kananan yara da ma balibai na kasashen Afirka 53 ta hannun kungiyar bunkasuwa ta matan shugabannin kasashen nahiyar, sun shiga hannun kungiyar, an kuma mika su ga kasashen kamar yadda aka tsara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China