2020-10-27 10:35:43 cri |
Tarayyar Afrika AU, ta ce kasancewar matasa 'yan kasa da shekaru 35 suka mamaye kaso 75 na al'ummar Afrika, wato sama da mutum biliyan 1.2, su ne suka fi rauni wajen fama da tasirin annobar COVID-19.
Wata sanarwa da AU ta fitar, ta ce a bana, annobar COVID-19 ta aukawa duniya, kuma yadda take ci gaba da yaduwa na kawo tsaiko ga harkokin yau da kullum a fannoni da dama, inda ta jaddada cewa, annobar na illa ga matasan nahiyar ta bangarori da yawa.
A cewar sanarwar, baya ga kasancewar matasan mafi fuskantar barazanar kamuwa da cutar COVID-19 tare da sauran al'umma, su ne kuma mafi rauni wajen fuskantar sauran abubuwan da cutar da kuma dabarun yakarta za su haifar.
Alkaluman da AU ta fitar, sun nuna cewa, sama da kaso 75 na al'ummar Afrika biliyan 1.2 'yan kasa da shekaru 35 ne, yayin da wasu miliyan 453 na al'ummar nahiyar, suka kasance tsakanin shekaru 15 zuwa 35.
AU ta bayyana matasa a matsayin jigon ajandar ci gaban nahiyar, tana mai nanata cewa, sakamakon ci gaban matasan na da matukar muhimmanci da sakamako mai dorewa ga makomar nahiyar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China