Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu na neman zuba jarin dala biliyan 62 a bangaren ababen more rayuwa
2020-11-04 10:22:49        cri
Yayin da aka yi hasashen tattalin arzikin kasar Afrika ta kudu zai ragu da kaso 8 a bana, shugaban kasar Cyril Ramaphosa, ya ce gwamnati za ta mayar da hankali kan gyara fasalin tattalin arziki da zuba jari a bangaren kayayyakin more rayuwa.

Yayin wani zaman tattaunawa kan shirin ayyukan more rayuwa, shugaban ya ce cikin shekaru 4 masu zuwa, suna fatan zuba jarin Rand triliyan 1 a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa.

Ya ce gwamnati ta shirya sake inganta tattalin arzikin, kuma tana maraba da sabbin masu zuba jari bayan mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar.

Ya ce muhimmin abun da ya kamata a yi shi ne, inganta zuba jari a bangaren kayayyakin more rayuwa da kuma tabbatar da aiwatar da su, yana mai cewa annobar ta kawo tsaiko ga harkokin tattalin arziki.

Shugaban ya kara da cewa, jarin zai mayar da hankali ne kan ayyuka daban-daban daga sabbin gine-gine zuwa gyara wadanda ke akwai.

A cewarsa, babban abun da suke mayar da hankali a kai shi ne, inganta samar da guraben ayyukan yi da tabbatar da harkokin kasuwanci na cikin gida sun amfana.

Bugu da kari, ya ce bankunan raya kasa, da na kasa da kasa da sauran cibiyoyin kudi sun bayyana sha'awarsu ta zuba jari a bangaren samar da ababen more rayuwar.

Ya ce dukkan bangarorin na da matukar muhimmanci ga bunkasa tattalin arziki, da rage tsadar gudanar da kasuwanci da inganta karfin kasar na takara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China