Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta kudu ya kara sassauta dokar kullen cutar COVID-19
2020-08-16 17:00:12        cri
Afrika ta kudu zata kara sassauta matakan kullen da kasar ta dauka sakamakon bullar annobar COVID-19 domin ba da damar farfado da harkokin kasuwanci da tattalin arziki, shugaban kasar, Cyril Ramaphosa ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatarwa jama'ar kasar a ranar Asabar.

Majalisar ministocin kasar ta amince da mayar da kasar zuwa mataki na biyu daga mataki na uku da take kai a halin yanzu, wanda zai fara aiki daga tsakiyar daren ranar Litinin, hakan na nufin za'a cire dukkan haramci da aka sanya ta fannin cigaba da harkokin kasuwanci da tattalin arziki yayin da mafi yawan kamfanonin kasar za su koma bakin aikinsu.

A cewar shugaban kasar, za'a dage dukkan haramcin da aka sanya na hana zirga zirga a tsakanin larduna, za'a bude gidajen sayar da abinci da barasa, sannan za'a dage dokar hana sayar da taba da giya, yayin da za'a bada damar taron ganawa da iyalai da ziyarce ziyarce a tsakanin jama'a.

An sassauta dokar ne bayan saukin yaduwar annobar da aka samu a cikin 'yan kwanakin baya bayan nan.

A makonni ukun da suka gabata, ana samu matukar raguwar sabbin adadin masu kamuwa da cutar daga 12,000 da ake samu a kullum zuwa 5,000, in ji Ramaphosa.

Ya kara da cewa, duk da irin kyakkyawan fatan da ake da shi, amma bai kamata mutanen kasar Afrika ta kudu su yi sakaci da matakan yaki da cutar ba.

Haka zalika, shugaba Ramaphosa ya ce, dokar haramta zirga zirga tsakanin kasa da kasa, da hana taruwar mutanen da suka zarce 50 har yanzu tana nan daram, kuma za'a tsawaita dokar yaki da annobar ta kasar har zuwa watan Satumba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China