Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu ta samar da na'urorin taimakon numfashi na farko
2020-08-01 17:06:45        cri
Kasar Afrika ta Kudu ta kammala kashi na farko na kera na'urorin taimakon numfashi, wadanda za su taimaka mata yaki da cutar COVID-19.

Ministan ciniki da masana'antu na kasar Ebrahim Patel ne ya bayyana haka a jiya, yayin wani taro kan COVID-19. Inda ya ce, a jiyan aka kammala harhada na'urorin, wanda wani bangare ne na guda 10,000 da aka yi oda da farko, da cibiyar binciken kimiyya da masana'atu ta kasar ta kera.

Yanzu, Afrika ta Kudu ita ce kasa ta 5 cikin jerin kasashen da suka fi yawan masu cutar, inda take da mutane sama da 480,00 da aka tabbatar sun kamu. A watan Afrilun da ya gabata ne ta kaddamar da wani shiri na rand miliyan 250, kwatankwacin dala miliyan 14.7 domin samar da na'urorin a kasar.

Baki daya, shirin zai samar da naurori 20,000.

Ebrahim Patel ya kara da cewa, ya kamata karancin na'urorin ya zaburar da kasashen Afrika wajen karfafa masana'antunsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China