2020-09-14 13:40:46 cri |
A 'yan kwanakin da suka gabata, alkaluman da gwamnatin Afirka ta Kudu ta fitar suka nuna cewa, yawan GDPn kasar, a rubu'i na biyu na shekarar bana ya ragu da kashi 51 %, raguwar da ba a taba ganin irinta ba a tarihin kasar. Wannan ne karo na 4 a jere da ake samun raguwar GDPn a cikin rubu'i hudu da suka gabata. Jami'in ya ce muhimmin dalilin da ya haifar da wannan raguwar, shi ne tsauraran matakan da aka dauka a kasar da nufin hana yaduwar COVID-19.
Mboweni wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi 13 ga wata, ya ce ana daukar tasirin hakan ga kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Afirka ta Kudu, a matsayin wata babbar barazana ga tattalin arziki da harkokin kudin kasar.
Kwanan nan, kamfanin ya kara ba da umarnin takaita wutar lantarki a duk fadin kasar. Kaza lika jami'in ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa, za ta kaddamar da wani aiki na hadin gwiwa don hanzarta saurin farfadowar tattalin arziki, ta yadda za a cika alkawarin da gwamnatin kasar ta dauka ga al'ummar ta. (Bilkisu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China