Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi kira da a hada kai don magance kalubalen da duniya ke fuskanta
2020-11-04 10:11:53        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana cewa sadaukar da kai da yin hadin gwiwa, shi ne babban makami wajen magance kalubalen da duniya ke fuskanta.

Zhang Jun ya ce, yanzu duniya ta kasance tamkar kauye daya. Yadda hadin kai ya dunkule kasashe waje guda, ya nuna cewa, dan-Adam yana da makoma ta bai daya. A don haka akwai bukatar, raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama, maimakon tunani na wasu kananan kungiyoyi ko rashin tunani ma baki daya.

Jami'in ya kuma shaidawa muhawarar manyan jami'an kwamitin sulhun MDD da aka kira game da " Masu haddasa tashin hankali da rashin tsaro" cewa, barazana da kalubalolin da duniya ke fuskanta, suna bukatar tsauraran matakai na kasashen duniya. Haka kuma wajibi ne kasashen duniya, su kare tsarin cudanyar bangarori daban-daban, su kuma karfafa rawar da MDD ke takawa.

Ya ce, har kullum kasar Sin ta yi imanin cewa, ya kamata dukkan kasashe manya ko kanana, su samu 'yanci da damammaki na bai daya, su kuma martaba dokokin da suka shafi harkoki na kasa da kasa. Haka kuma ya kamata, dukkan kasashe, su martaba dalili da manufofin tsarin MDD, su kiyaye tsarin kasa da kasa wadda MDD ke jagoranta, su kuma kiyaye odar kasa da kasa kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China