Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana da kafofin watsa labaru na kasashe da dama sun nuna yabo ga alkaluman tattalin arzikin Sin
2020-10-20 14:21:46        cri

Masana da kafofin watsa labaru na kasashe da dama sun mayar da hankali kan alkaluman tattalin arzikin kasar Sin na watanni tara na farkon bana da aka gabatar, suna ganin cewa, hakan na nuna farfadowar tattalin arzikin Sin, wanda zai sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya baki daya.

Masanin tattalin arziki na bankin OCBC na kasar Singapore Tommy Dongming Xie ya bayyana cewa, alkaluman tattalin arzikin Sin da aka gabatar sun shaida cewa, Sin ta samu farfadowa daga yanayin yaki da cutar COVID-19, kana bunkasuwar tattalin arzikin Sin za ta amfanawa farfadowar tattalin arzikin duniya.

Ministan kula da kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha na kasar Habasha Ahmedin Mohammed ya yi nuni da cewa, Sin ta yi nasarar farfado da tattalin arziki, ta samu ci gaba a fannonin ciniki ta yanar gizo, da ayyukan more rayuwa, da hidimar jigila, gwamnatocin Sin da kamfanonin ciniki ta yanar gizo na kasar sun kawo irin wannan ciniki ga kauyuka, wannan abu ne mai wuya ga sauran sassan duniya.

Jaridar The New York Times ta kasar Amurka ta bayar da labari cewa, a yayin da yawancin yankunan duniya suke yin kokarin tinkarar cutar COVID-19, Sin ta sake shaidawa duniya cewa, za a iya farfado da tattalin arziki cikin sauri idan aka cimma nasarar hana yaduwar cutar. Sin ita ce kasa ta farko da ta gabatar da karuwar alkaluman tattalin arzikinta bisa bara a duniya.

Darektan ofishin kula da harkokin kudi na asusun ba da lamuni na duniya Victor Gaspar ya yi tsammani cewa, gwamnatin kasar Sin ta nuna goyon baya sosai ga farfado da tattalin arziki. Yanzu haka, kasar Sin tana ci gaba da yiwa manufofinta na raya tsarin tattalin arziki gyaran fuska, wanda zai kara maida hankali ga samun bunkasuwa mai dorewa, da kula da rayuwar jama'a, da raya tattalin arziki bisa dogaro da bukatun cikin gida.

Mai nazari na cibiyar nazarin manyan tsare-tsaren duniya na birnin London na kasar Birtaniya David Ramirez ya bayyana cewa, farfadowar tattalin arzikin Sin ta shaida cewa, za ta kara shigar da kayayyaki daga sassan duniya, abu mai muhimmanci ga farfado da tattalin arzikin duniya, kuma Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayayyaki a duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China