Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane dubu 80 sun kamu da COVID-19 a rana a Amurka
2020-11-03 09:42:48        cri
Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Amurka (CDC) ta sanar a jiya Litinin cewa, sama da mutane dubu 80 ne aka ba da rahoton sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a duk rana a kasar, sabon matsakaicin adadin yawan mutanen dake kamuwa da cutar a kowace rana, tun barkewarta zuwa wannan lokaci.

Alkaluman cibiyar sun nuna cewa, matsakaicin yawan wadanda suka kamu da cutar a kowace rana a cikin mako guda da ya gabata ya kai dubu 80,800, kana wadanda cutar ta halaka ya kai 826 a duk rana, adadin dake karuwa tun karshen watan Satumba.

A cewar bayanan da jami'ar John Hopkins ta fitar, ya zuwa jiya Litinin da rana, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ta Amurka, ya haura miliyan 9.26, baya ga mutane sama da 231,300 da suka mutu sanadiyar cutar. Rahotanni na nuna cewa, a cikin kwanaki 14 kadai, an samu sabbin masu kamuwa da cutar miliyan 1 a kasar, daga mutane miliyan 8 zuwa miliyan 9. Karuwa mafi sauri, tun barkewar annobar.

Masanin cututtuka masu yaduwa na gwamnatin Amurka, Anthony Fauci, ya ce kasar tana cikin mawuyacin hali na tunkarar annobar cikin watanni masu zuwa. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China