Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: Wata mota ta aukawa kasuwa a jihar Ondo
2020-11-02 20:13:16        cri

A kalla mutane 16 ne suka rasu, baya ga wasu 7 da suka jikkata, lokacin da wata babbar mota ta kwace ta shiga kasuwa a Akungba Akoko dake jihar Ondo, a kudu maso yammacin Najeriya.

Kwamandan hukumar yaki da hadurra reshen jihar Boboye Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar hadarin a jiya Lahadi, cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi.

Oyeyemi ya ce, cikin mutane 23 da hadarin ya rutsa da su, 7 da suka hada da maza 3, mata 3, da yaro daya, sun ji raunuka daban daban, wadanda tuni aka garzaya da su asibiti. Kawo yanzu ba a tabbatar da dalilin kwacewar motar da ta haddasa wannan hadari ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China