Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da a kawo karshen cin zarafin jama'a da ake zargin 'yan sanda a Nijeriya
2020-10-22 09:21:49        cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kawo karshen cin zarafin da ake zargin 'yan sanda da aikatawa a Nijeriya.

Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ruwaito Sakatare janar din na cewa, bisa la'akari da yanayin da ake ciki a Nijeriya, yana kira da a kawo karshen cin zarafi da musgunawa da ake zargin 'yan sanda na yi a kasar.

Antonio Guterres, ya kuma yi tir da yadda rikici ya ta'azzara, ranar Talata a jihar Lagos, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da raunatar wasu da dama.

Ya kuma jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki. Har ila yau, ya yi kira ga hukumomin kasar da su gudanar da bincike kan aukuwar lamurran tare da hukunta wadanda ke da hannu.

Baya ga haka, ya bukaci jami'an tsaro a Nijeriya su rika gudanar da aikinsu ta hanyar kai zuciya nesa, yana kuma mai kira ga masu zanga-zanga su yi shi cikin lumana tare da kauracewa rikici.

Bugu da kari, ya karfafawa hukumomin kasar gwiwar gaggauta neman hanyoyin kawo karshen lamarin, inda ya jaddada cewa, a shirye MDD take ta mara baya ga kokarin kasar na samun mafita. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China