Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An cinnawa kafafen yada labarai wuta a zanga zangar Najeriya
2020-10-22 09:42:46        cri

Kimanin kafafen yada labaru uku aka cinnawa wuta a ranar Laraba, inda ake zargi wasu bata gari dake fakewa da zanga zangar neman kawo karshen cin zarafin jami'an 'yan sanda a jihar Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Gidan talabijin na jihar Lagos, mallakin gwamnatin jihar, da gidan talabijin na TVC, wanda ke watsa shirye shiryensa a tsawon sa'o'i 24 ko wace rana, da kuma jaridar The Nation, wacce ake wallafa ta a kullum, wadanda ke yankuna daban daban a jihar ta Lagos, wasu bata gari sun afkawa gidajen jaridun, kamar yadda tashar yada labarai ta Channels Television ta rawaito.

Rahotanni sun ce, gidan talabijin na TVC yana tsaka da gabatar da shirye shiryensa ne sai bata garin suka kutsa kai cikin harabar gidan talabijin din, suka cinnawa motocin dake gidan wuta da sauran kayayyakin ma'aikata, da baki, da kuma tashar talabijin din.

Harin ya haifar da gidan talabijin din ya katse shirye shiryensa. Sai dai ba a ba da rahoton samun hasarar rayuka ba.

An samu rahotannin tashe tashen hankula a wasu biranen Najeriyar yayin da bata gari suka yi amfani da zangar zangar neman yin garambawul a tsarin 'yan sandan kasar suka tada rikici.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China