Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a samar da rundunar musamman ta ko ta kwana don kai dauki a lokacin barkewar rikici
2020-11-01 15:55:46        cri

A yayin da take bayyana damuwarta game da karuwar barazanar zaman lafiya da tsaro da makomar ci gaban Afrika wanda matsalolin ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi ke haddasawa, majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bukaci a samar da cikakkiyar rundunar musamman ta ko ta kwana ta Afrika wato ASF, domin kai dauki a kan lokaci kan duk wata barazanar tashin hankali da ta tasu a nahiyar.

Wannan mataki ya zo ne bayan taron da aka gudanar na bayan bayan nan na majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta AU game da kafa sashen musamman na yaki da ayyukan ta'addanci karkashin rundunar musamman ta ASF.

Majalisar ta nanata cewa, hukumar AU da hukumar raya tattalin arzikin shiyyar, sun jaddada aniyarsu ta samar da kakkarfar tawagar tsaro ta ko ta kwana, da kuma samar da isassun kudade, da kwararru, domin yin amfani da su wajen tabbatar da cikakkiyar kariya da tsaron Afrika.

Sanarwar ta ce, majalisar ta jaddada muhimmancin musayar kwarewa, da yin amfani da darrusan da aka koya daga nahiyar wajen yaki da ta'addanci da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da sauran laifuffuka a nahiyar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China