Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babbar cibiyar shuka 'ya'yan itatuwa dake kusa da kogin rawaye
2020-10-29 15:40:34        cri

Ma Wenming, shi ne mai kula da manyan rumfunan shuka 'ya'yan itatuwa dake kauyen A'yihai a yankin Hainan dake lardin Qinghai. Ya ce, cikin wadannan manyan rumfuna, ana shuka pitaya a galibin gonakin, domin pitaye shi ne 'ya 'yan itatuwa na farko da aka shigo da su cikin kauyen, shi ya sa, suna da kwarewa wajen shuka pitaya sosai.

A shekarar 2016, Ma Wenming ya halarci wani kwas na horaswa kan ayyukan gona a birnin Zhangye na lardin Gansu, cikin wannan kwas, ya yi mamaki kwarai da gaske ganin yadda ake noman pitaya sosai a birnin. Sa'an nan, ya yi nazari kan yanayin kasa dake tsakanin kauyensa da birnin Zhangye, yana ganin cewa, yanayin wuraren biyu suna kama da juna, shi ya sa, ya fidda wannan ra'ayi na shuka pitaya a kauyensa.

A shekarar 2017 kuma, ya fara shuka pitaya a babbar rumfa ta gidansa, sa'an nan, ya fara girbi pitaya a shekarar 2018. Wannan nasarar da ya cimma, ya sa ya zuba jari Yuan dubu 400 wajen gina manyan rumfuna guda 7 domin shuka pitaya.

Bisa kokarin da shi da uwargidansa suka yi, pitayar da suka shuka sun fara yin suna a sassa daban daban, hakan ya sa, sun sayar da dukkanin pitaya da suka fitar. Ma Wenming ya ce, a bana, ya sami kudin shiga har Yuan dubu 400 ta hanyar sayar da pitaya.

Yanzu, ya fara samar da guraben ayyukan yi ga masu fama da talauci a wurin, kowane mutum zai iya samun kudin shiga Yuan 3600 a kowane wata, lamarin da ya samar da wadata ga karin mutane masu shuka pitaya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China