Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta ba da gudummawa wajen kawo karshen talauci a duniya
2020-10-29 19:55:52        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya fada cewa, kasarsa ta himmatu wajen ba da gudummawarta wajen rage talauci a duniya, da kuma yin amfani da matakai na zahiri don taimakawa sauran kasashe masu tasowa cimma burinsu na kawar da talauci.

Wang ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Alhamis a nan Beijing, inda ya kuma nuna cewa, kullum al'ummar Sin na kokarin cimma burin "ganin bayan yunwa a fadin duniya." Ya kara da cewa, kasar Sin ta taimaka wajen gina cibiyoyin gwajin fasahohin aikin gona 24 a Afirka, inda mutane fiye da 500,000 dake yankin suka amfana. A cewar rahoton Bankin Duniya, tare da hadin gwiwar raya ayyukan more rayuwa a fannin zirga-zirgar dake bin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", ana sa ran za a taimaka wa mutane miliyan 7.6 fita daga kangin talauci da kuma mutane miliyan 32 fita daga matsakaicin talauci.

Wang ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta aiwatar da jerin matakan da shugaba Xi Jinping na kasar ya sanar a yayin muhawarar babban taron MDD karo na 75, don ba da sabuwar gudummawa a kokarin da ake na kawar da talauci da samun ci gaba a duniya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China