Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan ta kara farashin mai a kasar
2020-10-28 11:36:44        cri
A jiya Talata gwamnatin kasar Sudan ta yanke shawarar ninka farashin mai a kasar, wanda ya fara aiki nan take.

Khairy Abdel-Rahman, mai rikon mukamin ministan makamashi da hakar ma'adanar na kasar, ya bayyana a taron manema labarai a Khartoum, babban birnin kasar cewa, gwamnati ta yanke shawarar kara farashin mai ga masu motocin da ba na haya ba kuma masu jigilar fasinja a kasar. Ministan ya ce, za a dinga sayar da litar man gas a kan Fam 46 na kudin kasar ga masu motocin kansu, yayin da motocin haya za su dinga biyan Fam 106 kan kowace lita na kudin kasar. Shi kuwa man Benzine za a dinga sayar da lita a kan Fam 56 ga motocin masu zaman kansu, yayin da motocin haya za su dinga biyan Fam 120 kan kowace lita. Sabon farashin man zai fara aiki ne tun daga yammacin ranar Talata.

Gwamnatin rikon kwaryar Sudan tana gudanar da sauye-sauye wanda ta cimma matsaya da asusun bada lamuni na IMF, wanda ya kunshi har da batun cire tallafin man gas da na benzine. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China