Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da gudunmuwar shinkafa ton 1500 da nufin tallafawa shirin zaman lafiya a Sudan ta kudu
2020-10-27 10:25:12        cri

Gwamnatin kasar Sin ta tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya na Sudan ta kudu, ta hanyar ba da gudunmuwar ton 1,500 na shinkafa domin taimakawa hadin kan dakaru.

Za a yi amfani da gudunmuwar da aka ba kwamitin rikon kwarya na kasar wajen ciyar da dubban sojojin dake sansanonin daban-daban a fadin kasar ta gabashin Afrika.

Ministan kula da wanzar da zaman lafiya na kasar, Stephen Pal, ya ce tallafin na kasar Sin zai gaggauta hada kan rundunonin sojin kawance.

Ya ce a madadin gwamnati da al'ummar Sudan ta Kudu, yana bayyana matukar godiya ga al'umma da gwamnatin kasar Sin, bisa taimakonsu ga tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Jakadan kasar Sin a Sudan ta Kudu, Hua Ning, ya ce tun daga bara, Sin ta taimakawa shirin wanzar da zaman lafiya na kasar da tantuna 2,500 da barguna 50,000 da shinkafa ton 3,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China