2020-10-26 09:47:48 cri |
Mahukunta a kasar Sudan, sun sha alwashin fadada dangantaka da Amurka a fannoni da dama wadanda za su amfani al'ummun sassan biyu, bayan da Amurkan ta tsame Sudan din daga jerin kasashe masu taimakawa ayyukan ta'addanci.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Sudan din ta fitar ce ta bayyana hakan, tana mai cewa, amincewar da gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi, ta cire Sudan daga jerin sunayen kasashen da ake zargi da tallafawa ta'addanci, ta bude wani sabon babi na hadin gwiwar kasashen 2.
Hakan zai kuma baiwa Sudan damar sake kulla kyakkyawar alaka da sassan kasa da kasa, tare da tallafawa farfadowar tattalin arzikin ta, bayan mummunan tasirin da ya fuskanta, lokacin da kasar ke cikin jerin wadancan kasashe da aka sanyawa takunkumi
Bugu da kari, ma'aikatar ta jaddada aniyar Sudan, ta yin aiki tukuri a fannin yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China