Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan da Masar da Habasha za su koma tattaunawa game da madatsar GERD
2020-08-17 09:55:05        cri

A gobe Talata ne kasashen Sudan da Masar da Habasha, suka amince za su koma tattaunawa game madatsar ruwa ta GERD, wadda kasar Habasha ke ginawa a kogin Nilu.

Hakan dai ya biyo bayan taron ranar Lahadi da Afirka ta kudu ta kira ta kafar bidiyo, inda ministocin harkokin wajen kasashen uku suka amince da ci gaba da tattaunawa a gobe 18 ga wata.

Wata sanarwa da ministan albarkatun ruwa na kasar Sudan ya fitar, ta ce mahalarta taron na fatan amfani da taron na gaba, wajen hade sassan yarjeniyoyin da sassan uku suka gabatar.

Sanarwar ta kara da cewa, Sudan ta jaddada jajircewar ta game da komawa teburin shawarwari bisa salon hadin kai na kasashen Afirka, karkashin ajandar da aka amincewa a baya, da tanajin dokokin kasa da kasa masu nasaba da raba albarkatun ruwa ba tare da cutar da juna ba.

A shekarar 2011 ne dai kasar Habasha ta fara ginin madatsar ta GERD, wadda ake sa ran za ta rika samar da sama da megawatt 6,000 na lantarki, wanda hakan zai habaka ci gaban kasar.

A hannu guda kuma, Masar da Sudan, wadanda su ma ke da iyaka da kogin Nilu, kuma suke amfana daga ruwan sa, ke ci gaba da nuna damuwa cewa madatsar ta GERD za ta rage musu gajiyar da suke samu daga kogin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China