2020-09-25 10:06:18 cri |
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar cewa, an hallaka wasu daga cikin manyan kwamandojojin kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram a lokacin aikin sintirin da sojojin Najeriyar suka kaddamar a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.
A wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin rundunar tsaron kasar John Enenche ya ce, dakarun sojojin dake da babban sansanin a yankin Malamfatori, a kwanan nan sun kaddamar da gagarumin aikin murkushe 'yan ta'adda a yankunan tafkin Chadi, inda suka yi nasarar tarwatsa sansanoni da mafakar 'yan ta'addan a wurare daban daban kimanin biyar dake yankin karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Ya ce aikin da sojojin suke gudunawar na hadin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro, abin yabawa ne a kokarin kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda da ma sauran kalubalolin tsaro dake addabar kasar.
Ya bukaci mazauna yankunan shiyyar arewa maso gabashin kasar, su ci gaba da baiwa jami'an tsaron hadin kai wajen ba su gamsassun bayanai kuma a kan lokaci wadanda za su taimaka musu gudanar da ayyukansu.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China