Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kiyaye farfado da tattalin arzikin Sin zai sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya
2020-10-21 14:29:56        cri

Alkaluman da kasar Sin ta fitar a ranar 19 ga wata, na nuna cewa yawan GDP na kasar a rabi'un farko ya ragu da kashi 6.8 cikin dari bisa makamancin lokacin bara, kana adadin ya karu a rabi'un biyu da kashi 3.2 cikin dari, kuma yawansu a rabi'un uku ya karu da kashi 4.9 cikin dari. Don haka, GDP na kasar a cikin wannan shekara ya karu daga raguwar da ya samu a baya, lamarin da ya jawo hankalin kafofin watsa labaru na kasa da kasa sosai.

Kafar watsa labaru ta CNN ta kasar Amurka ta bayar da labari cewa, bayan da Sin ta samu karuwar kaso 3.2 na tattalin arziki a rabi'u na biyu, tattalin arzikinta ya ci gaba ta karuwa da kashi 4.9 cikin dari a rabi'u na uku, wannan ya shaida cewa Sin ta kiyaye farfado da tattalin arziki bayan abkuwar cutar COVID-19. Musamman a yayin da sauran kasashen duniya suke fuskantar matsalolin tattalin arziki da tinkarar cutar COVID-19 tare, farfadowar tattalin arzikin Sin ta zama abin misali a duniya.

Yawancin kafofin watsa labarun kasa da kasa na ganin cewa, tattalin arzikin Sin ya farfado ne, sakamakon daukar managartan matakan yaki da cutar COVID-19 da kuma fadada fannoni daban daban na farfado da tattalin arzikin kasar. Kana kiyaye farfadowar tattalin arzikin Sin zai sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China