Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sanya dokar hana fita a jihar Lagos dake Najeriya
2020-10-21 10:03:05        cri

Mahukunta a jihar Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya sun sanya dokar hana fita ba dare ba rana, tare da sanar da rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu, sakamakon kazancewar boren kin jinin cin zarafin da 'yan sanda ke yiwa jama'a.

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa, yana cewa, daukar matakin zai taimaka wajen magance bazuwar tashin hankali, yayin boren neman kawo karshen rundunar yaki da ayyukan fashi da makami (SARS) da aka rusa a farkon wannan wata.

Gwamnan ya ce, an sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a dukkan sassan jihar, tun daga ranar Litinin din da ta gabata, sai dai dokar ba ta shafi masu gudanar da ayyuka na musamma, da masu kai dauki ba.

An sanya dokar ce, a matsayin wani mataki na kandagarki don tabbatar da tsaron dalibai, da gine-gine da iyaye, yayin da ake ci gaba da samun karuwar boren nuna adawa da yadda 'yan sanda ke musguwa jama'a.

Rahotanni na cewa, mutane da dama ne suka jikkata yayin zanga-zangar da ta barke a wasu manyan biranen kasar a 'yan kwanakin nan ciki har da 'yan sanda.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China