Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tura dakarun kwantar da tarzoma na musammam zuwa sassan kasar
2020-10-21 09:56:46        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, babban sifeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu, ya ba da umarnin tura rundunar kwantar da tarzoma ta musamman zuwa dukkan sassan kasar, don kare rayuka da dukiyoyin al'umma daga ayyukan bata gari, biyo bayan boren kin jinin musgunawar da 'yan sanda ke yiwa jama'a.

Mai magana da yawun rundunar Frank Mba, ya bayyana cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe cewa, wuraren da aka tura 'yan sandan kwantar da tarzoman, sun hada da manyan gine-ginen gwamnati da gidajen yari dake sassan kasar. Wannan umarnin na zuwa ne, yayin da ake samun karuwar kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati da na jama'a a wasu sassan jihohin kasar, ciki har da Abuja, babban birnin kasar.

Mba ya kara da cewa, an bukaci manyan jami'an 'yan sandan jihohi, da su gano, da gaggauta kama masu zanga-zanga dake karya doka, su kuma hukunta irin wadannan bata gari a helkwatocinsu.

A cewarsa, ya zuwa yanzu an kama mutane 12 da ake zargi da hannu da kai hare-hare da lalata ofisoshin 'yan sanda a birnin Benin na jihar Edo dake yankin kudancin Najeriya. Yana mai cewa, an kuma yi nasarar kwato bindigogi kirar AK47 da a baya aka sace, a lokacin da wasu bata gari suka barnata wasu ofisoshin 'yan sanda a sassan kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China