Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta sanar da gagarumin shirin yaki da ta'addanci a duk fadin kasar
2020-10-18 15:41:13        cri
Hukumomi a Najeriya sun sanar da kaddamar da gagarumin shirin sojoji na yaki da matsalar rashin tsaro a duk fadin kasar, hukumar sojojin kasar ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Kakakin sojojin Najeriyar, Sagir Musa ya ce, shirin na wannan shekara wanda aka yi wa lakabin "CROCODILE SMILE", wani bangare ne na yunkurin sojojin kasar don dakile matsalar tsaro a kasar ta yammacin Afrika.

Shirin sintirin sojojin zai shafi dukkan sassan kasar dake fama da matsalolin rashin tsaro, wanda ya hada har da amfani da shafukan intanet wajen ganowa, da bibiyar dukkan masu yada munanan kalamai ta kafafen sada zumunta na zamani da ma dukkan shafukan intanet a kasar.

Kakakin hukumar sojojin ya ce, wannan ne karon farko da aka fara amfani da wani tsari na tabbatar da tsaro ta shafukan intanet a tarihin rundunar sojojin Afrika.

Za a fara aikin ne daga ranar 20 ga watan Oktoba zuwa 31 ga watan Disamba.

A cewar jami'in, aikin ya kuma shafi yadda za a samar da wani tsarin gano mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram da suke tserewa daga shiyyar arewa maso gabashin kasar zuwa wasu yankunan kasar sakamakon matsin lambar da suke fuskanta na hare-haren da sojojin ke kaddamarwa kansu musamman a arewa maso gabashi, da arewa ta tsakiya, da kuma arewa maso yammacin Najeriya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China