Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 4 sun mutu, 8 sun ji rauni a ruftawar gini a Najeriya
2020-10-12 10:36:30        cri
Mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu, wasu mutanen 8 sun samu raunuka a yayin da wani gani mai hawa uku wanda ba a kammala aikin ginawa ba ya rufta a ranar Lahadi, a Legas cibiyar kasuwancin Najeriya.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Legas, LASEMA, tace har yanzu ba a tantance hakikanin musabbabin faruwar hadarin ba wanda ya afku a yankin Obalende a birnin Legas.

Ya zuwa yanzu, jami'an aikin ceto sun gano gawarwakin mutane hudu wanda ya hada har da mace guda, a cewar Nosa Okunbor, kakakin hukumar ta LASEMA, wanda ya kara da cewa, mutanen 8 da suka samu raunuka an gargaza da su asibiti mafi kusa.

Mazauna yankin dake makwabta da wajen sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, duk da kasancewar gini ne wanda ba a kammala shi ba, amma akwai mutane da yawa dake zaune cikinsa gabanin ruftawar ginin.

Wani mazaunin wajen Olalekan Kayode ya ce, ana fargabar mai yiwuwa ne ginin ya danne wasu mutanen, ko da yake, har yanzu masu aikin ceto suna cigaba da gudanar da aikinsu domin zakulo mutanen da iftila'in ya rutsa da su.

Ya kara da cewa, wasu daga cikin mutanen da hadarin ya rutsa da su mazauna kusa da wajen da ginin ya rufta ne.

Hukumomi sun bayyna cewa suna cigaba da gudunar da bincike domin gano musabbabin hadarin.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China