Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sean Conley: Trump ba ya dauke da cutar COVID-19
2020-10-13 10:07:08        cri
Likitan fadar White House ta Amurka Sean Conley, ya ce sakamakon gwajin baya bayan nan da aka yi wa shugaba Donald Trump, ya nuna yanzu ba ya dauke da kwayoyin cutar COVID-19.

Shugaban na Amurka ya kwashe kwanaki 12 ke nan, tun bayan da likitoci suka tabbatar ya harbu da cutar ta COVID-19 a ranar 1 ga watan Oktoba, inda ya shafe kwanaki 3 yana jinya a asibiti. Mr. Conley ya ce bayan kammala yi masa gwaji, yanzu haka Trump ya warke, kuma ba zai yiwu ya yada cutar ga wani ba.

Tuni dai shugaba Trump ya tsara gudanar da ganganin yakin neman zabe a Sanford na jihar Florida da almurun yau Litinin, gangamin da zai zamo na farko da zai halarta, tun bayan harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19.

An samu ma'aikatan fadar White House da dama da suka kamu da wannan cuta, kafin da ma bayan harbuwar shugaba Trump da ita.

Yanzu haka dai saura kwanaki 22 a kada kuri'u a zaben shugabancin Amurka, inda tuni aka fara jefa kuri'u na wurwuri a wasu jihohin kasar, a gabar da yawan Amurkawa da suka harbu da COVID-19 ya kai miliyan 7.8, alkaluman da kafar watsa labarai ta NBC ta ce ana hasashen za su karu, zuwa sama da mutum miliyan 8 nan da ranar Alhamis mai zuwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China