Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Amurka 3500 sun ki yarda da karbar karin haraji kan kayayyakin kasar Sin
2020-09-27 15:22:43        cri

Wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gabatar a jiya Asabar, ya ce, cikin makonni 2 da suka wuce, kamfanonin kasar Amurka kimanin 3500 sun shigar da kara a kotu, bisa zargin matakin da gwamnatin shugaba Trump ta dauka, na karbar karin haraji kan kayayyakin kirar kasar Sin, wadanda darajarsu ta zarce dalar Amurka biliyan 300, da cewa ya saba doka.

Wadannan kamfanonin sun hada da Volvo dake samar da manyan motoci, da kamfanin Pep Boys mai hada kayayyakin mota, da kamfanin Ralph Lauren mai samar da tufafi, da dai sauransu.

Cikin kararrakin da suka shigar a kotun dake kula da batun cinikin kasa da kasa ta kasar Amurka, suna zargin wasu jami'ai da hukumomin kasar Amurka da yunkurin ta da rikici ta fuskar ciniki, tsakanin kasashen Amurka da Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China