Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka za ta saka wa bankunan Iran 18 takunkumi
2020-10-09 11:59:16        cri
A jiya Alhamis, kasar Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu bankuna 18 na kasar Iran.

Sai dai ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ya yi Allah wadai da babbar murya da wannan mataki na kasar Amurka, inda ya ce gwamnatin kasar Amurka na neman toshe hanyoyin kasar Iran na biyan kudi don musayar abinci da magunguna, yayin da ake fama da cutar COVID-19 a kasar. A cewarsa, yunkurin kasar Amurka na jefa jama'ar kasar Iran cikin yunwa, wani babban laifi ne na keta hakokkin bil Adama.

A watan Yulin shekarar 2015, kasar Iran ta kulla yarjejeniya tare da bangarorin Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha, da Sin, da Jamus, kan yadda za a daidaita batun nukiliyar kasar, inda aka kayyade cewa, kasar Iran za ta takaita shirinta na kera makaman nukiliya, yayin da gamayyar kasa da kasa, a nasu bangare, za su soke takunkumin da aka sanya wa kasar. Sai dai daga bisani, kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar bisa radin kanta, a watan Mayun shekarar 2018, ta sake kakabawa kasar Iran takunkumi. Lamarin da ya sanya kasar Iran ita ma ta sanar da daina martaba wasu bangarori na wannan yarjejeniyar, tun daga watan Mayun shekarar 2019. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China