Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta kafa sabbin cibiyoyin raya tattalin arziki don bunkasa ma'adinai
2020-10-09 10:11:53        cri
Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin kafa sabbin cibiyoyin raya tattalin arzikin na musamman domin bunkasa fannin ma'adinai da kuma samar da guraben ayyukan yi masu yawan gaske, wani babban jami'in hukumar fitar da kayayyaki zuwa ketare NEPZA ya bayyana hakan.

Adesoji Adesugba, manaja daraktan hukumar ta NEPZA ya ce, wannan shiri wani bangare ne na alkawarin da gwamnatin kasar ta dauka na bunkasa fannin ma'adinai domin fadada hanyoyin samun kudaden shigar kasar, kamar yadda ya bayyana cikin wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ya ce an tsara kafa cibiyoyin raya tattalin arziki na musamman guda hudu a jihohin Legas, Gombe, Kwara da Kastina, inda za a bada fifiko kan ma'adinai.

Adesugba ya ce, idan an kafa wadannan cibiyoyin hudu za su taimaka wajen farfafdo da fannin ma'adinai da kuma samar da guraben ayyukan yi ga matasa, kana gwamnatin kasar za ta samu hanyoyin samun kudaden shiga ta hanyar fitar da albarkatun zuwa kasashen ketare. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China