2020-10-09 10:03:30 cri |
Bayan kammala taron majalisar zartaswar kasar na wannan mako a Abuja, a ranar Laraba, ministan sufuri Rotimi Amaechi, ya fadawa 'yan jaridu cewa, aikin gina sabon layin dogon da kayayyakin taragun jiragen na dakon kaya, zai lashe kudin dala biliyan 3.02.
Ministan ya bayyana cewa, taron majalisar ministocin ya kuma amince da aikin gina sabuwar tashar tsakiyar teku a Bonny, wato tashar mai a yankin kudancin Najeriya, da kuma gina rukunin kamfanin jiragen kasa a Fatakwal.
Amaechi ya ce, za a gina sabon reshen layin dogon wanda zai hade tashar fatakwal, da kamfanin man Najeriya zuwa Bonny wanda ya kunshi tashar tsakiyar teku da kuma ta Owerri, wata cibiyar samar da kayan amfanin gona a kasar. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China